Mace ta zama Bishop a cocin Ingila

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nadin ya janyo rarrabuwa tsakanin 'yan Anglican

Cocin Ingila ya nada mace a matsayin Bishop a karon farko a cikin tarihinsa.

An yi bikin nada Rabaren Libby Lane a matsayin Bishop ta yankin Stockport, watanni shida bayan cocin ya kada kuri'ar kawar da tsohon tsarin nada Bishop maza zalla.

Rabaren Libby Lane ta ce tana fatan nadinta ya bai wa mata damar cika burinsu na rayuwa.

Batun nada mata a matsayin Bishop ya janyo rarrabuwa tsakanin kiristoci mabiya akidar Anglican, a yayinda masu ra'ayin gargajiya suke adawa da tsarin.

Lane 'yar shekaru 48, tana da 'ya'ya biyu kuma mijinta ma limamin coci ne.