An dage dokar hana fita a Maiduguri

Yan Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yan Boko Haram

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ta dage dokar hana fita da ta kafa a birnin Maiduguri babban birnin jihar Borno sakamakon harin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai da nufin kwace birnin.

Wata majiya ta tsaro ta shedawa BBC cewar sai da maharan suka sake kai farmakin a birnin, amma sojojin Nijeriya suka fatattake su.

Hukumar kula da agajin gaggawa ta Nigeriya NEMA ta ce, kura ta lafa a fafatawar da ake yi da 'yan Boko Haram a Maidugurin sai dai kuma 'yan gudun hijira daga Munguno na kara kwarara cikin birnin.

Daruruwan 'yan gudun hijira daga garin Munguno na jihar Borno wanda ya fada hannun 'yan Boko Haram a harin da suka kai jiya a garin da birnin Maiduguri da nufin kwace wuraren biyu, na cigaba da tururuwa suna shiga birnin Maiduguri don neman mafaka.

Wani dan kato-da-gora watau Civilian JTF ya ce a daren jiya an kai gawarwakin mutanen Munguno da dama da aka kashe a asibitin Maiduguri, kuma wadanda suka samu raunuka sun ce, 'yan Boko Haram da suka mamaye garin suna cigaba da kone gidajen mutane.

Hukumar kula da agajin gaggawa ta kasa a Nijeriyar NEMA ta ce babu alkaluma na yawan mutanen dake shiga Maiduguri a yanzu, saboda tana cigaba da karbar su.

Mohammed Kanar, babban jami'in hukumar mai kula da shiyyar arewa maso gabashin Nijeriyar ya ce, an rigaya an tanadar musu kayan bukatu da suka hada da abinci.

Karin bayani