'Boko Haram' ta bude shafin Twitter

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Boko Haram ta kashe dubban mutane a Nigeria

Wani shafin Twitter da ke ikirarin magana da yawun kungiyar Boko Haram ya wallafa wasu hotunan yara kanana da ake bai vwa horon kan yadda za su yi yaki.

An wallafa hotunan yaran ne dauke da makamai a ranar Lahadin da ta gabata jim kadan bayan hukumomin Nigeria sun bayar da sanarwar cewa sun dakile hare haren Boko Haram a Maiduguri.

An wallafa hotunan ne a shafin na Twitter mai suna Al- Urwatul- Wuthka.

Shafin ya kuma bayar da bayanai kan wasu fafatawa da 'yan Boko Haram din suka yi da sojoji a garuruwa daban-daban.

Da ma dai sojojin Nigeria sun jima suna zargin 'yan kungiyar da amfani da kananan yara a matsayin sojin yaki.

Amfani da kananan yara dai babban laifi ne a dokokin yaki na duniya.