Turkey ta nemi Facebook ya rufe wani shafi

Shafin Facebook Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shafin Facebook

Gidan radiyon BBC ya samu labarin cewa kamfanin Facebook ya kiyaye da wata doka ta Kotun Turkiyya wadda ta nemi a rufe wani shafi wanda tace ya saba ma Annabi Muhammad {S.A.W}.

Idan kamfanin na sada zumunta ya ki bin wannan umurni, Kotun ta yi barazanar rufe kafar shiga shafin na Facebook baki-dayan sa.

Wannan shafi yana da mabiya kimanin miliyan 40 a kasar ta Turkiyya.

Kamfanin sada zumuntar na Facebook ya ki cewa uffan kan batun, to amma yana da tsayayyar manufa ta rufe wani bangare na shafinsa a cikin wata kasa muddin dai ya saba ma dokar kasar.

Kamfanin na Facebook ya buga wani rahoto na bukatar da gwamnatoci a sassa dabam-dabam na duniya suka gabatar na neman bayanan masu mu'amalla da shi.

Rahoton baya-bayan nan wanda ya kama daga watan Janairu zuwa watan Yuni na shekara ta 2014 ya nuna cewar an haramta duba wasu bayanai har 1;893 a shafin na Facebook a Turkiyya a wannan lokacin.

Haka kuma a a wanan lokacin, a wani takaitaccen lokaci Turkiyyar ta rufe shafukka na Twitter da Youtube.

Wadannan kamfanonin za su iya zamowa da hedikwata ne a Amurka, to amma masu mu;'amalla da su dukkan mutanen duniya ne - dole ne su kiyaye tare da mutunta dokokin kasashe da al'adu kamar yadda wani kwararren masanin harkar tsaro ta internet Farfesa Alan Woodward daga Jami'ar Surrey ya ambata.

Akwai dai hadari ga gwamnatin da take sa ido tare da tace abinda mutanen kasa ke gani, don haka kamata ya yi a sanar da mutanen idan gwamnatin tana sa ido kan wannan abu.

A cewar kungiyar kare hakkin dan adam Amnesty International, a yanzu haka ana binciken daya daga cikin manyan jaridun kasar Cumhuriyet na aikata miyagun laifukka saboda ta buga wasu hotuna daga mujallar nan ta Faransa Charlie Hebdo sakamakon kisan wani ma'aikacin ta.

Karin bayani