Ana cire pastocin siyasar Nijeriya a Ghana

Shugaba Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

A kasar Ghana a 'yan kwanakin da suka wuce ne rassan manyan jam'iyyun siyasar Nijeriya da ke Ghana wato PDP da APC suka kakkafa manyan allunan alamominsu wato poster, a wasu sassan birnin Accra, a kampen din da suke yi na jan hankalin magoya bayansu da su je gida Nijeriya su kada kuri'a a lokacin zaben kasar da za'a gudanar a cikin watan gobe.

Sai dai tun a karshen makon da ya gabata ne hukumomin birnin na Accra suka fara tunbuke manyan allunan postocin a wuraren da suka girke su.

Hukumomin kasar sun bayar da umurnin a tumbuke pastocin ne saboda dalilan tsaro.

Masu sharhi kan al'amurran yau da kullum a kasar ta Ghana sun ce matakin nan ya yi daidai, saboda ganin yadda siyasar Nijeriyar ta yi zafi. Idan rikici ya barke, zai iya shafar kasar Ghana.

Karin bayani