IS ta yi barazanar kashe dan kasar Japan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mista Abe ya ce Japan tana aiki tare da Jordan domin ganin an sako Mista Goto

Firayi ministan Japan ya yi Allah wadai da wani sabon hoton bidiyo da kungiyar IS ta fitar, inda suke barazanar kashe wani dan kasar Kenji Goto cikin sa'o'i 24.

Mr. Shinzo Abe ya ce kasar sa tana aiki tare da Jordan domin ganin mayakan kungiyar ta IS sun sako mutumin.

A cikin bidiyon, an ji wata murya da aka yi amanna ta Kenji Goto ne yana cewa za a kashe shi tare da wani matukin jirgin sama dan kasar Jordan, muddin ba a saki wata 'yar kasar Iraki da aka yanke wa hukuncin kisa a Jordan ba.

Mr. Abe ya kuma bukaci majalisar dokokin kasar data dauki dukkan matakan da suka dace domin kare 'yan kasar dake zaune a gida da wasu kasashe.

Ita dai matar, Sajida Al-Rishawi, 'yar kungiyar Al'qaeda ce, wadda mahukuntan kasar Jodarn suka yanke wa hukuncin kisa saboda hannu da take da shi a wani hari da aka kai a 2005 wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 60.