Bincike kan kashe jami'in leken asirin Rasha

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kashe Litvinenko ya janyo cece-kuce tsakanin Biritaniya da Rasha

An fara gudanar da wani bincike a Biritaniya game da kisan wani tsohon jami'in leken asirin Rasha, Alexander Litvinenko wanda aka yi a London.

Rundunar 'yan sandan Biritaniya ta ce an kashe tsohon jami'in hukumar KGB ne da gubar nukiliya ta Polonium a 2006.

Ya kasance wanda yake gaba-gaba wajen sukar gwamnatin Rasha.

Lauyan hukumar binciken ya ce an gano burbushin sinadarin Polonium a sassa daban-daban na wuraren Mr Litvinenko ya ziyarta kafin rasuwarsa.

Rasha dai ta musanta hannu a kisan nasa.