An yi kutse a intanet din jirgin Malaysia

Jirgin Malaysia MH370
Image caption Kamfanin jirgin na kokarin farfadowa daga ibtila'in da ya afka masa na batan jirgin MH370, da kuma harbo MH17 da 'yan aware magoya bayan Rasha suka yi a gabashin Ukraine.

Masu satar bayanai sun yi kutse a Intanet din kamfanin jirgin saman kasar Malaysia.

Sai dai kamfanin ya sanar da cewar abin bai shafi masu mu'amala da shi da suka sayi tikitinsu ta shafin ba, haka kuma ba su yi nasarar satar bayanan kamfanin ba.

Hakan na zuwa ne yayin da kamfanin jirgin dai na kokarin farfadowa daga bala'in da ya fada masa na batar jirgin nan MH370 da ke dauke da fasinjoji sama da 300.

Sannan da harbo jirgin Malaysia MH17 a gabashin Ukraine, inda 'yan tawaye magoya bayan Rasha suka mamaye a bara.

A ranar litinin ne aka sauya hoton da ke babban shafin kamfanin, inda aka rubuta '' Ba a gano jirgi mai lamba 404 ba''.

Lambar 404 ita ake samu a duk lokacin da aka so bude shafin amma kuma sai na'urar kwamfutar ta yi tutsu, amma masu satar bayanan sun kai amfani da ita ta wata fuskar daban.

Haka kuma an wallafa hoton kadangare sanye da hula da taba a bakinsa, haka kuma an yi amfani da sunan kungiyar masu fafutukar kafa daular musulunci a kassahen Iraqi da Syria wato ISIS a shafin.

Sai dai har yanzu ba a bayyana dalilin da ya sa masu kutsen ta internet din suka far wa shafin na kamfanin jirgin sama na Malaysia ba, kuma ba a bayyana dangantar da ke tsakanin kungiyar ISIS da masu satar bayanan ba.