Boko Haram: EU ba za ta aika da masu sa ido ba

Image caption Hukumar zabe ta ce za ta gudanar da zabuka a yankin.

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce ba za ta tura jami'anta arewa maso gabashin Najeriya domin sanya idanu kan zabukan da za a gudanar ba.

Kungiyar ta ce ta dauki wannan mataki ne saboda rashin tsaron da yankin ke fama da shi.

Kungiyar dai ta yi kira da a kyautata tsaro a yankin.

Hukumar zaben kasar dai ta ce za ta gudanar da zabe a yankin duk da matsalolin rashin tsaro da ake fuskanta.

A cewar hukumar, mutanen da suke gudun hijira sanadiyar hare-haren da 'yan kungiyar boko Haram ke kai wa a yanki za su samu damar kada kuri'unsu a sansanoninsu.