Alibaba ya yi sa'insa da hukuma a China

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kamfanin Alibaba shi ne kan gaba a hada hadar saye da sayarwa ta intanet a China

Katafaren kamfanin saye da sayarwa ta intanet na kasar China, Alibaba ya yi sa'insa da daya daga cikin hukumomin dake sa ido a kan hada hadarsa.

Sa'insar ta taso ne sakamakon zargin kamfanin Alibaba da gazawa wajen dakile cinikayyar da ta saba doka ta shafinsa.

Kamfanin ya maida martani inda ya zargi hukumar dake sa idon da yin kure, tare da cewa zai shigar da nashi korafin.

Kimanin masu saye miliyan 279 da masu sayarwa miliyan 8 da rabi ne ke amfani da shafin intanet na kamfanin Alibaba.

A cikin makon daya gabata mutumin da ya samar da kamfanin Alibaba, Jack Ma ya sanar da kudurin su na kara yawan masu mu'amala da kamfanin zuwa biliyan 2 ta hanyar fadafa ayyukansa a duniya.

A halin yanzu, kamfanin Alibaba yana barazana ga takwarorinsa eBay da Amazon da ire-irensu.