An gargadi dakarun Nigeria kafin harin Baga

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram sun yi barna sosai a Baga

Sabbin hujjoji sun nuna cewa an gargadi jami'an tsaron Nigeria a kan yiwuwar kai hari daga 'yan Boko Haram a Baga da kuma Monguno amma kuma ba su dauki wani mataki ba.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International wacce ta yi zargin ta ce rundunar Nigeria ta gaza wajen kare fararen hula abin da ya janyo hasarar rayuka da dama.

Wani babban jami'in tsaro ya ce shaidawa Amnesty International cewar kwamandan sansanin soji a Baga ya bayyanawa shalkwatar tsaron Nigeria a cikin watan Nuwamba da Disamba cewa suna fuskantar barazana daga Boko Haram kuma har ya nemi karin jami'an soji zuwa yankin.

Wasu majiyoyin da kuma shaidu sun bayyana cewa sojoji a Monguno sun samu gargadi tun da wuri a kan cewa 'yan Boko Haram za su kowo musu hari a ranar 25 ga Junairu.

"A bayyane take cewar shugabanin sojin Nigeria sun yi kasa a gwiwa wajen kare fararen hula a Baga da Munguno duk da gargadin da aka yi musu a kan harin Boko Haram," in ji Netsanet Belay, Daraktan Amnesty International a Afrika.

A farkon wannan watan ne 'yan Boko Haram suka kaddamar da hari a Baga da Doron Baga inda suka hallaka mutane da dama tare da kona gidaje fiye da 3,000.