Facebook ya bayyana ribar dala miliyan 701

Facebook
Image caption Ribar da kamfanin Facebook ya samu ta wuce yadda aka kiyasta

Kamfanin Facebook ya bayyana samun ribar dala miliyan 701 a watanni ukun karshe na shekarar da ta gabata.

Hakan kuma na nufin kamfanin ya samu karin kashi 34 ke nan cikin kashi dari.

Kudaden tallace-tallace sun karu da kashi 53 cikin dari, wato kwatankwacin dala miliyan 3.59, wanda daga nan ne kamfanin ya fi samun ribar.

Mafi yawan tallace-tallacen wadanda suke fitowa ne ta wayoyin salula.

Yanzu haka kamfanin na tunkaho yana da masu ziyartar shafin da yawansu ya kai biliyan 1.39 a kowane wata, wato an samu karin kashi 13 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar da ta wuce.

"Mun yi abubuwa da dama a shekarar 2014" In ji Mark Zuckerberg a wata sanarwa da kamfanin ya fitar.

Ribar da kamfanin ya ci a shekarar ta 2014 baki daya ta kama dala biliyan 2.9 kusan ninkin wacce aka samu a shekarar 2013.

Sai dai kamfanin ya koka kan yadda hada-hadar kudaden a Amurka ya shafi samun ribar, wadda kamfanin ya ce da ta fi haka.