Hizbullah ta kashe sojin Isra'ila a wani hari

Isra'ila da Hizbullah

Isra'ila ta ce an kashe sosjojinta biyu a wani hari da kungiyar 'yan Shi'a ta Hezbollah ta kai kan jerin gwanon motocin sojinta a kan iyakar kasashen biyu.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce an raunata bakwai daga cikin dakarun nata.

Tuni dai Isra'ila ta maida martani wajen yin lugudan wuta a kan wasu sassan kudancin Labanon.

Kakakin Firaministan Isra'ila, Mark Regev, ya ce kasarsa za ta kare kanta daga duk wata barazana:

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe daya daga cikin dakarun wanzar da zaman lafiyarta a Labanon, amma ba ta yi bayani kan yadda al'amarin ya wakana ba.

Hezbollah dai ta ce harin ramuwa ne kan wani harin sama da Isra'ila ta kai Syria, wanda ya yi sanadiyar mutuwar wani Janar na kasar Iran da kuma da yawa daga mayakan kungiyar kwanaki goma da suka wuce.