Mutane 12 sun mutu a wani hari a Mali

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rikicin 'yan tawayen Azbina ya dade yana addabar arewacin Mali

Rahotanni daga arewacin kasar Mali na cewa kimanin mutane 12 ne suka rasa rayukansu, bayan wani harin da wasu masu dauke da makamai da ke goyon bayan gwamnati suka kai kan wasu 'yan tawayen Azbinawa.

Bayanai na nuna cewa har da 'yan kunar bakin wake a cikin wadanda suka kai harin na Tabankort.

Masu aiko da rahotanni sun ce ba abu ne da aka saba gani ba a Mali, ace dakarun gwamnati sun yi amfani da 'yan kunar bakin wake.

A ranar Talata ne mutane uku suka mutu a wata zanga-zangar da aka yi a garin Gao a wajen sansanin dakarun Majalisar Dinkin Duniya.