'A soke dokar batanci ga addini a duniya'

Wata hadakar kungiyoyi da ke fafutukar kare hakkin bil adama ta ce za ta kaddamar da yakin ganin an soke dokar nan da ke hukunta masu nuna batanci ga addini.

Masu fafutukar sun ce ganin yadda harin da aka kai a kan mujallar Charlie Hebdo da ke Faransa, lokacin ya yi da za a kawar da dokar.

Kungiyoyin sun kuma yi gargadin cewa harin na tauye hakkin bayyana ra'ayi tare da bai wa masu kai hare-hare mafaka.

Kasashe da dama da ke amfani da dokar sun ce dokar na da muhimmanci domin tana kare muzgunawa masu addinai.

Kasar Saudi Arabia wacce ke da tsauraran hukunci a kan batanci ga addini na so ne a kara tsawaita dokar.