Castro ya bukaci Obama ya dage takunkumi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mista Castro ya ce rashin dage takunkumi zai kawo tarnaki ga farfado da huldar diflomasiya

Shugaban kasar Cuba ya yi kira ga shugaba Obama na Amurka da ya yi amfani da karfin ikonsa, ya mance da majalisar dokokin kasar, ya cire takunkumin huldar tattalin arziki a kan Cuban.

Mista Raul Catsro ya kuma bukaci Amurkan da ta mayar da kurkukun Gwantanamo Bay hannun Cuba, domin rashin yin hakan zai kawo tarnaki ga farfado da huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Wannan shi ne jawabin Shugaba Castro na farko tun bayan tattaunawa mai cike da tarihi tsakanin jami'an Amurka da na gwamnatin Cuba a Havana cikin makon jiya.

Jawabin na Shugaba Catsro jaddada matsayar kasarsa ne akan wasu abubuwan da kasashen biyu suka ja layi akai da dadewa.

Abu na farko shi ne cire takunkumin tattalin arziki da Amurka ta kakaba wa Cuba tsawon shekaru 50, sannan abu na biyu, mayar da kurkukun Gwantanamo Bay ga Cuban.