IS: Japan na nazarin sabuwar muryar da aka fitar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan kungiyar IS sun bai wa Japan da Jordan wa'adin zauwa faduwar rana

Hukumomi a kasar Japan na ci gaba da yin nazarin wata murya da aka nada, wadda ake ikrarin ta dan jaridan kasar ne da 'yan kungiyar IS suke garkuwa da shi.

Har ila yau muryar ta yi barazanar kashe matukin jirgin kasar Jordan da kungiyar ke tsare da shi.

Kungiyra ta IS ta ce mudddin hukumomin Jordan din ba su saki matar nan 'yar kasar Iraqi da ake zargi na da hanu a harin bam din da aka kai a Amman shekaru goma da suka gabata ba babu makawa sai sun kashe matukin jirgin.

Kasar Jordan ta ce a shirye take ta yi musayar fursunoni muddin aka ba ta tabbacin cewa matukin jirgin yana da rai.