Ba za mu zabi Jonathan ba - 'Yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan gudun hijirar sun ce ba za su yarda da yaudarar Jonathan ba

Wasu 'yan gudun hijirar Najeriya da ke samun mafaka a Jamhuriyyar Nijar sun ce babu wata yaudara da shugaba Jonathan zai yi musu har su zabe shi.

Ranar Talata ne dai gwamnatin Najeriyar ta aika musu da tallafin kayan abinci da na kwanciya, sai dai kayan na dauke ne da hotunan shugaba Jonathan.

An kai kayan ne ga hukumomin Jamhuriyar ta Nijar domin mika su ga 'yan gudun hijirar.

Sai dai wasu da BBC ta tattauna da su sun ce hakan wani salo ne na yakin zaben shugaba Jonathan don haka ba za su karbi kayan abincin ba.

Wani daga cikinsu ya ce, "ba ma son kayan abincin kwata-kwata ba ma bukata. Idan da yana son mu da zai yi mana wani abu a kan matsalar tsaron da muke fama da ita".

Sai dai wakilin Najeriya a Nijar, Ambasada Aliyu Musa Sakkwato, ya ce gwamnati ta kai wa 'yan gudun hijirar tallafi ne domin rage musu radadin da suke ciki, amma ba don siyasa ba.

Jami'an gwamnatin Nigeriar sun ce an sanya hotunan Shugaba Jonathan a jikin tallafin ne a matsayinsa na shugaban kasa ba don yana takara ba.