A kama tsagerun Naija Delta - TY Danjuma

Hakkin mallakar hoto ireporter
Image caption Tsohon jagoran 'yan taratsin Niger Delta, Asari Dokubo

A Najeriya, tsohon ministan tsaron kasar, Janar Theophilus Danjuma, ya bukaci hukumomin tsaro su kama tsofaffin tsagerun Niger Delta saboda barazanar da suka yi cewa idan ba a sake zaben Goodluck Jonathan ba za su yi sanadiyar wargajewar kasar.

Janar T.Y. Danjuma ya ce ire-iren wadannan kalamai ba su da kan gado, kuma bai kamata gwamnati ta kyale mutane su rika yin su ba.

Tsohon ministan -- daya daga cikin dattijan kasar ne -- ya ce wasu kalaman da 'yan siyasa suke furtawa a yakin neman zabe suna da matukar hadari.

Janar Danjuma ya ce ya kamata 'yan siyasar su sanya wa bakunan su linzami.

Hukumomin tsaro

A makon jiya ne dai tsagerun Niger Deltan suka yi taro a gidan gwamnan jihar Bayelsa -- mahaifar shugaba Jonathan -- inda suka ce ba za a zauna lafiya a kasar ba idan ba a sake zaben Mr Jonathan ba.

Sai dai hukumomin tsaro dai ba su kama su ba, ba kuma su gayyace domin yi musu tambayoyi ba kan barazanar, wanda masu sharhi ke cewa ka iya yin sanadiyar tayar da hankali.

A baya dai hukumomin tsaro sun kama 'yan hamayya saboda yin kalaman da suka ce na tayar da hankula ne, lamarin da wasu 'yan kasar ke gani na da alaka da siyasa.