Ebola ta ragu a Yammacin Afrika - WHO

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane fiye da dubu shida ne dai suka mutu sakamakon annobar ta Ebola

Hukumar lafiya ta duniya ta ce yawan sababbin mutanen da suka kamu da cutar Ebola ya ragu zuwa kasa da 100 a makon jiya.

Alkaluman mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar su ne mafi karancin da aka samu tun a watan Yuni.

A cewar hukumar matakan da ake dauka yanzu sun zama na dakile cutar a maimakon rage yaduwarta a yammacin Afrika.

Masana kimiyya da ke bibiyar yadda cutar ta ke a kasar Guinea sun ce kwayoyin cutar sun rikida tun bayan gano cutar a watan Maris din shekarar 2014.