Ba ni da hannu a Boko Haram – Jonathan

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Jonathan ya ce nan ba da dadewa ba zai magance matsalar ta Boko Haram

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce ba shi da hannu a hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kai wa a arewacin kasar.

Shugaban, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake yakin neman zabe a Yola, babban birnin jihar Adamawa ya ce mahaukaci ne kawai zai yi tunanin cewa mutum kamar sa na da hannu a hare-haren na Boko Haram.

Mista Jonathan ya ce a shekarar 2011 kuri'un da ya samu a jihar ta Adamawa sun ninka wadanda ya samu a jiharsa ta Bayelsa, "don haka ko da a siyasance, hakan [daukar nauyin Boko Haram] kamar cakawa cikina wuka ne".

Shugaban Jonathan ya bukaci 'yan jihar ta Adamawa su kara hakuri, yana mai cewa nan ba da dadewa zai kawar da kungiyar ta boko Haram.

Sai dai duk da wadannan kalamai da Mista Jonathan ya yi a Yola, wasu mutane sun jefi ayarin motocinsa.

Jihar ta Adamawa dai na cikin jihohin da aka sanya wa dokar ta-baci sakamakon hare-haren da Boko Haram ke kai wa.