Google zai sauya tsarin kare bayanan sirrin jama'a

Google Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kamfanin Google ya amince ya sauya tsarin kare bayanan sirrin jama'a

<span >Kamfanin Google ya amince zai sauya tsarin kare bayanan jama'a bayan da ya samu matsin lamba daga ofishin kula da bayanai na Burtaniya.

An bukaci Google ya saukaka hanyoyin da masu amfani da shafukan ke bi wajen ganin yadda ake tattara bayanan su.

Hakan na faruwa ne bayan da aka gudanar da wani bincike, kuma ana kan gudanar da irin wannan sauye-sauye a wasu sassan nahiyar turai.

Ana kuma kyautata zaton kamfanin na Google zai samar da irin wannan shirin sauye-sauye a wasu kasashe da dama.

Bincike da ofishin kwamishina mai kula da bayanai a Burtaniya, ya gano cewa, Google bai fayyace yadda ake tattara bayanan jama'a.

Yanzu haka kamfanin na Google na daga nan har zuwa 30 ga watan Yuni na wannan shekara domin ya aiwatar da sauye - sauyen.

Ana kuma sa ran kamfanin zai fitar da wani tsari na bai daya a nahiyar ta turai.