Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Rikicin Siyasa a Najeria

Nan da makonni biyu ne idan Allah ya kaimu za a yi zaben gama-gari a Nageria. Sai dai tun yanzu an fara nuna fargaba a kan yiwuwar barkewar rikici.

An samu rahotannin jifar tawagar Jam'iyyar PDP da take yakin neman zabe a wassu jihohin... Yayin da kuma jamiyyar APC mai adawa ta ce an kona mata ofishin yakin neman zabe a Jihar Rivers.

Kuma a makon jiye ne wasu magoya bayan shugaban kasar, Goodluck Jonathan suka ce za su tada yaki a kasar muddin shugaban ya fadi a zaben da za a yi.

Yaya aka yi zaben kasar ya kasance da gaba haka? Kuma ta yaya za a kauce wa rikici a lokacin zaben da kuma bayan an kammala shi?