Dakarun Nigeria sun kwato Michika - Jonathan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Garuruwa biyar ne dai kungiyar ta Boko Haram ta karbe a jihar Adamawa

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya ce dakarun kasar sun kwace garin Michika daga hannun 'yan Boko Haram a jihar Adamawa.

Inda ya kara da cewa gari daya da ya rage a hannun 'yan kungiyar, wanda kuma ya sha alwashin cewa shi ma za a kwato shi ne Madagali.

Mr. Jonathan ya bayyana hakan ne a yayin yakin neman zaben da ya je a birnin Yola, a ranar Alhamis.

Ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya za ta hada hannu da gwamnatocin jihohi wajen sake gina muhallan da aka lalata a yayin rikicin Boko Haram.