Baga: An fara tuhumar sojojin Nigeria

Nigeria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana tuhumar sojojin ne bisa sakaci da ake zargin su nuna a lokacin harin Baga

Rundunar sojin Nigeria ta fara tuhumar wasu manya- manyan jami'an soji bisa zarginsu da sakaci a harin da Boko Haram ta kai garin Baga a jihar Borno.

Cikin jami'an sojin da aka kama sun hada da Birgediya janar, laftanal kanal da kwamanda da kuma Janar.

Ko da yake kakakin rundunar sojin Nigeria, Chris Olukolade ya shaida wa BBC cewa duk bayan wani babban aikin soji, kowane jami'i na yin bayani game da abin da ya faru.

Rahotanni sun ce ana tsare da jami'an ne a Maiduguri bisa zarginsu da kasa dakile harin da 'yan Boko Haram suka kai, abin da ya kai kungiyar kwace sansanin dakarun kawance da ke garin na Baga.