An tuhumi kamfanin Uber a kotun Amurka

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Direban kamfanin Uber ya yi wa wata 'yar kasar Indiya fyade

Wata mata 'yar kasar Indiya wadda ta ce direban kamfanin Uber a Delhi ya yi mata fyade, ta shigar da kara a wata kotun Amurka inda ta ke tuhumar kamfanin.

Matar mai shekaru 26 ta zargi kamfanin Uber da kasawa wajen kare fasinjojin da ke mu'amala da kamfanin, inda ta bukaci a biya ta diyya.

A cikin wata sanarwa, kamfanin Uber ya ce yana bai wa hukumomi hadin kai domin tabbatar da an hukunta direban da ya tafka aika aikan.

A halin yanzu, direban mai suna Shiv Kumar Yadav ya na fuskantar shari'a bisa zarginsa da aikata laifin garkuwa da mutun da kuma fyade.

Matar ta ce direban ya tafi da ita wani kebabben wuri, sannan ya yi mata fyade.

Sai dai direban ya musanta wannan zargi.

Lauyan matar ne ya shigar da karar a San Francisco, inda shedkwatar kamfanin ta ke.

A farkon watan Disamban bara ne hukumomin Delhi suka hana kamfanin Uber da wasu kamfanonin safa masu aiki da intanet ci gaba da harkokinsu saboda sun kasa yin kyawawan gwaje-gwaje akan direbobinsu.