Amurka ta kashe wani jigon kungiyar IS

US Hakkin mallakar hoto
Image caption Amurka ta ce kashe Abu Malik zai gurgunta ayyukan IS

Amurka ta ce ta kashe wani kwararre a fannin hada makamai masu guba dake aiki da kungiyar IS mai da'awar kafa daular musulunci.

An samu nasara kashe mutumin mai suna Abu Malik a wani harin sama da aka kai na hadin gwiwa a Iraqi.

Kasar ta Amurka ta bayyana cewa mutuwar Abu Malik za ta gurgunta damar da kungiyar ta IS ke da ita na hada makaman.

Akwai rahotanni dake cewa mutumin ya taba aiki a karkashin tsohon shugaban kasar Iraqi Saddam Hussien, a matsayin mai hada makamai masu guba, kafin Amurka ta mamaye kasar a shekarar 2003