Ebola: An dage sake bude makarantu a Liberia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A farko, gwamnatin Libera ta tsayar da ranar Litinin domin sake bude makarantu

Gwamnatin kasar Liberia ta sanar da jinkirta sake bude makarantu a kasar, wanda aka shirya yi ranar Litinin, bayan cutar Ebola ta tilastawa hukumomi rufe makarantun a bara.

Ko da yake ana samun raguwar masu kamuwa da cutar yanzu a kasar, gwamnatin ta ce har yanzu, makarantu ba su shirya komawa akin aiki ba.

Makarantu da asibitoci, wurare ne da ake kamuwa da cutar Ebola a Liberiya, a saboda haka aka rufe dukkan makarantu lokacin da cutar ke ganiyar yaduwa.

A halin yanzu, an shawo kan yaduwar cutar, sai dai da yawan makarantun ba su shirya komawa bakin aiki ba.

Babu wasu kayayyakin kare dalibai daga kamuwa da cutar, kamar ruwan wanke hannu dake dauke da sinadaran kashe kwayar cutar Ebola da na'urorin gwada cutar ebola a jikin dalibai.