IS sun fillewa dan jaridar Japan kai

Shugaban Japan Shinzo Abe Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Japan ta matukar fusata da kisan da aka yi wa Mr Goto.

Japan ta bayyana matukar bacin ran ta game da kisan da aka yi wa dan kasar Kenji Goto da masu tada kayar baya na kungiyar IS suka yi.

Prime Minista Shinzo Abe ya kira kisan da mummunan aiki ne , ya kara da cewar Japan ba za ta taba yafewa wadanda suka aikata kisan ba kuma za ta ci gaba da aiki da kasashen duniya dan yakar masu tada kayar baya da ke ikirarin kafa daular musulunci.

Shi ma ministan tsaron Japan ya bayyana sahihancin hoton bidiyon da aka nuna yadda aka fillewa Mr Goto kai.

Tun bayan sace Kenji mahaifiyarsa ke rokar mayakan IS su taimaka su sake shi, a yanzu da hoton bidiyon ya nuna yadda aka kashe shi ta shiga mawuyacin hali.

Kenji Goto wanda dan jarida ne, an sace shi ne a kasar Syria a watan Octobar shekarar da ta gabata, a lokacin da ya ke kokarin ganin an saki dan kasar Japan da aka yi garkuwa da shi wanda kuma mayakan IS suka fillewa kai a makon da ya wuce wato Haruna Yukawo.