AU:Za ta dora haraji kan tikitin jirgin sama

A karshen taron kolin su na kwanaki biyu shugabannin kungiyar tarayyar Afirka sun bada shawarar sanya haraji a wani yunkuri na samar da kudaden gudanar da harkokin kungiyar.

Sun bada shawarar dora haraji akan tikitin jirgin sama da otel-otel da kuma gajeren sakonnin na wayar salula wato text messages a turance.

A baya dai tsohon shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi shine ya samar da makudan kudade na tafiyar da kungiyar, amma a yanzu tana samun kudade ne mafi akasari daga kasashen duniya masu bada taimakon jin kai.

Shugabanni a taron kolin a Addis Ababa sun kuma bukaci kotun duniya mai shari'ar manyan laifuka ta soke tuhuma akan shugaban Sudan Omar al-Bashir da mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto.