Sojojin Chadi sun ce sun kai hari Gamboru

Sojojin Chad Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Chad

Rahotannin baya-bayan nan sun nuna cewar sojojin Chadi sun kai wa 'yan Boko Haram hari a Gamborun gala na jahar Borno a kan iyaka da kasar Kamaru a arewa masu gabashin nijeriya.

'Yan kungiyar dai sun yi kaka-gida ne a garin tun wata da watanni da suka wuce, bayan da ya fada hannunsu.

Rahotanni dake fitowa daga yankin na cewa an ga 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram suna cika rigunansu da iska suna barin garin na Gambarou, a yayin da mutanen kauyukan suke cikin farin-ciki da murna game da faruwar wannan lamari.

To, sai dai a wani sako da aka wallafa ta shafin twitter dake ikirarin magana da yawun Boko Haram, kungiyar ta ce ta mayar da martani kan harin da sojojin na Chadi da na Kamaru suka kai mu su a garin na Gamborou.

Karin bayani