Za a fara gwajin riga-kafin Ebola a Liberia

Allurar riga kafin cutar Ebola. Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Cutar Ebola ta hallaka mutane sama da dubu tara a kasashen Guinea, da Liberia da kuma Saliyo.

A ranar Litinin ne za a fara gwaji mafi girma na riga-kafin cutar Ebola a kasar Liberia.

An dai shigar da allurar riga-kafin cikin kasar cike da matakan tsaro, sannan aka kai su wurare na sirri.

Ana kuma sa ran kusan mutane 30,000 da suka sadaukar da kan su ne za a yi wannan gwajin riga kafin a kansu.

Kamfanonin GSK da Merck ne suka samar da allurar riga-kafin.

Masana kimiyya na Amurka da Liberia da ke cikin aikin yin riga-kafin sun ce za a yi wa ma'aikatan sa kan allurar 'yar mitsitsiyar kwayar cutar Ebola a jikinsu, kuma wani likita dan kasar da shi ma yake cikin wadanda za a yi wa allurar ya ce babu hadari idan aka yi hakan saboda sinadarin da yake cikin riga-kafin ba zai haifar da cutar Ebolar ba.

A cikin shekara guda da babbar annobar cutar Ebola ta barke, kusan mutane dubu tara ne suka rasa rayukansu, yawancinsu a kasashen Guinea da Liberia da kuma Saliyo.