Ba zan fita daga PDP ba —Sule Lamido

Gwamnan Jiagawa Alhaji Sule Lamido. Hakkin mallakar hoto google
Image caption Gwamnan dai yace ya na nan daram a jam'iyyarsa ta PDP.

A jiya ne aka yi wata ganawar sirri ta tsahon sa'o'i biyu tsakanin gwamnan jihar Rivers Chibuke Rotimi Amechi wanda har ila yau shi ne babban darakta na kwamitin yakin neman zabe na dan takarar Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari a jam'iyyar adawa ta APC.

Da gwamann jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido shi ma daraktan yakin neman zaben shugaba Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP a shiyyar Arewa maso yammacin Nigeria.

Gwamna Rotimi Amechi ne ya yi tattaki zuwa birnin Dutse domin yin wannan ganawa.

Babu dai wani bayani game da abubuwan da gwamnonin biyu suka tattauna a kai, to amma wasu na ganin anya kuwa ba ta da nasaba da sauya shekar gwamna Sule Lamido zuwa jam'iyyar adawa ta APC ba?

Sai dai Alhaji Sule Lamidon ya musanta hakan, ya na mai cewar ko babu komai tun da can a jam'iyyar guda suke da Mr Amechi, dan haka bai ga abin tsegumi ba dan ya kawo masa ziyara.

Haka nan ya nanata cewar me jam'iyyar adawa ta APC za su yi da shi, su da suke masa kallon kazami kuma arne dan haka ya na nan daram a jam'iyyarsa ta PDP.