Nigeria: Harin kunar bakin wake a Gombe

Hakkin mallakar hoto AP

Hukumomin tsaron dai na ci gaba da sintiri a cikin birnin yayin da mahukunta suka haramta hawa babura tun daga yau zuwa ranar Laraba sabo da abinda suka kira dalilai na tsaro.

Bayanai sun ce bama-baman na kunar bakin wake an tada su ne a wurare biyu a cikin birnin na Gombe mintuna kalilan a tsakaninsu.

Hari na farko ya faru ne a wani shataletale da ake kira Kuros a tsakiyar birnin, kana hari na biyu kuma a wata kasuwar Katako.

Kakakin rundunar 'yansandan jihar Gombe DSP Fwaje Attajiri, ya ce 'yan kunar bakin wake na harin farko wani namiji ne ya goyi wata mace akan Babur, wadanda bam din ya tarwatse da su.

Akalla biyar ne suka rasa rayukansu kana wasu takwas suka jikkata a hare-haren biyu.

kuma duka wadannan ka iya kasancewa wani babban sako ga Nijeriya yayin da kasar ke shirin gudanar da zabuka nan da kasa da makwanni biyu.