An gurfanar da Uber gaban kuliya

Wata matashiya na amfani da internet a India. Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kamfanin ya yi alkawarin tabbatar da an hukunta direban tasin.

Wata mata 'yar India ta ce wani direban tasi na kamfanin Uber da ake hayar mota ta shafin sa na Internet a birnin Delhi ya yi mata fyade.

Matar mai shekaru 26, ta zargi kamfanin da gazawa wajen tattabatar da tsaron fasinjojin da suke shiga motar su, ta na kuma bukatar a biya ta wasu kudade kan wanan abu da aka mata.

A na sa bangaren Uber yace ya na aiki kafada da kafada da hukumomi domin tabbatar da an hukunta wanda ake zargi idan an same shi da laifi.

Direban mai suna Shiv Kumar dai a yanzu haka ana tuhumarsa da laifin aikata fyade ga wata matar ta daban, da kuma zargin satar mutane.

Matar dai ta ce Mr Kumar ya kai ta wani wuri da babu zirga-zirga jama'a ne ka na ya yi mata fyade, sai dai ya musanta wannan zargi.

Lauyan ta ya shigar da karar ne a birnin San Francisco inda cibiyar kamfanin Uber ta ke, ya kuma bukaci kotun ta sakaya sunan matar.

A wata sanarwa da Uber ta fitar ta bakin kakakin kamfanin, Nairi Hourdajian ta ce kamfanin ya nuna matukar damuwa ga wannan abu da ya faru, tare da jajantawa wadda lamarin ya shafa, da kuma alkawarin tabbatar da cewar an yi mata adalci wajen yankewa direban hukunci daidai da laifin da ya aikata.