Sauyin yanayi ne ke haddasa ambaliyar ruwa

Yankin da Ambaliya ta shafa a Brittaniya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yankin da Ambaliya ta shafa a Brittaniya

Jama'a a Brittaniya na cigaba da alakanta sauyin yanayi ta wani bangare da ambaliyar ruwa da aka samu a shekara ta 2013.

Damuwar kusan ta koma ne ga hauhawar ambaliyar ruwan da aka ba da rahoto a shekara ta 2005, kamar yadda masu bincike a Jami'ar Cardiff suka nuna.

'Yan Brittaniyar da dama sun danganta sauyin yanayin da cewar babbar matsala ce dake addabar Brittaniya kafada-da-kafada da miyagun laifukka da batun ilimi a wani nazari na kasa da aka gudanar.

Mutane da dama suna kallon sauyin yanayin a matsayin abinda ya kara sanyawa ake samun ambaliyar ruwan, musamman ma kuma yadda ta shafe su kai-tsaye.

Sai dai kuma duk da yake akwai shedar da ta nuna zafin sauyin yanayin yana kara zama jiki, masana kimiyya sun ce abu ne da ba zai yiwu ba a alakanta sauyin yanayin da mutane dabam-dabam ke harare ga sauyin yanayin da za a hakikance ana samu.

Iska da ruwan sama mai karfi da aka fara samu cikin watan Oktoba na shekara ta 2013, ya tilasta ma mutane da dama yin kaura daga gidajensu kuma ya sanya ana kallon shekara ta 2013-14 a matsayin yanayi mafi laima da aka taba samu a tarihi.

An sake yin wani nazarin kan mutane dari 9 da casa'in da 5 a yankuna 5 da ambaliyar ruwa ta shafa a yankunan Ingila da Wales, hade da Dawlish da Gloucester da Aberystwyth, Hull da wasu sassa na kogin Thames da aka samu ambaliya.

Kusan 9 daga cikin mutane 10 sun amsa cewar lallai akwai alamu na sauyin yanayi, kuma kusan dukkansu sun yi imanin cewar ta wani bangare mutane ne da kan su ke haddasa shi.

Karin bayani