Ba zan huta ba sai an saki abokaina — Greste

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Iyalan Greste sun bukaci a saki sauran 'yan jarida

Iyalan dan jaridar nan na Aljazeera dan kasar Australia wanda aka sako daga gidan yarin Masar bayan ya kwashe kwanaki 400, Peter Greste, sun ce ba zai huta ba har sai an saki abokan aikinsa da ake ci gaba da tsarewa.

Sun bayyana haka ne a wani taron manema labarai da suka yi a Brisbane.

Mahaifin dan jaridar ya nuna rashin jin dadinsa da tsarewar da hukumomin Masar ke ci gaba da yi wa 'yan jaridar biyu: Mohamed Fahmy da Baher Mohamed.

An daure 'yan jaridar uku ne bisa zargin taimaka wa kungiyar 'Yan Uwa Musulmi wadda gwamnatin kasar ta Masar ta haramta da kuma wallafa labaran karairayi.

Sai dai dukkaninsu sun musanta zarge-zargen.