An kai hari kusa da gangamin Jonathan a Gombe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A jihar Gombe ne mace ta fara kai harin kunar bakin wake a Najeriya

Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu a wani harin da aka kai a jihar Gombe, jim kadan bayan shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kammala gangamin yakin neman zabe.

Rahotanni sun nuna cewa wata 'yar kunar bakin wake ce ta tarwatsa kanta kusa da filin wasan da aka yi gangamin na PDP, lamarin da ya janyo jikkatan wasu mutane 18.

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Gombe, DSP Fwaje Atajiri ya tabbatar da aukuwar lamarin.

A ranar Lahadin da ta wuce ma an kai harin kunar bakin wake sau biyu a jihar ta Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya.