Murar tsuntsaye na kara bazuwa a Nigeria

Illar Murar Tsuntsa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu kiwon kaji sun yi asarar miliyoyin naira sakamakon bullar cutar a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce cutar murar tsuntsaye ta bazu zuwa jihohi 16 na kasar.

A wajen wani taron manema labarai da ya kira ranar Litinin a Abuja, Ministan lafiya na kasar, Dr. Haliru Alhassan, ya ce har yanzu ba a samu wani mutum da ya kamu da cutar a kasar ba.

Sai dai kuma rahotanni daga sassa daban-daban na Najeriyar sun nuna cewa cutar ta hallaka dubban kaji a kasar.

A farkon watan Janairu ne cutar ta bulla a kasar, inda ta fara bulla a jihohin Kano da kuma Lagos.

Karin bayani