Sojoji sun yi luguden wuta a dajin Sambisa

Image caption Dakarun Nigeria na fuskantar kalubale daga kungiyar Boko Haram

Bayanai sun nuna cewa dakarun Nigeria sun yi luguden wuta a sansanin 'yan Boko Haram da ke dajin Sambisa a jihar Borno.

Kakakin rundunar tsaron Nigeria, Chris Olukolade, ya shaida wa BBC cewa tun a daren ranar Talata suka soma yi wa 'yan Boko Haram luguden wuta a Sambisa da kuma wasu wuraren da suke da sansanoni.

Rahotanni sun ce an yi amfani da jiragen yaki ne a wani yunkurin murkushe ayyukan 'yan Boko Haram.

A karshen mako, mayakan Boko Haram sun kai hare-hare a Maiduguri da Gombe da kuma Potiskum inda suka hallaka mutane da dama.

Rikicin Boko Haram ya raba mutane fiye da miliyan uku daga muhallansu a jihohi da dama na Nigeria.

A yanzu haka dai kungiyar Boko Haram ce ke iko da garuruwa da dama na arewa maso gabashin kasar.

Gabanin zabukan Nigeria da ke tafe nan da wasu 'yan kwanaki, Nigeria na bukatar tsaro domin kare masu kada kuri'a daga shiga cikin hadari.