Burtaniya ta amince mutane uku su haifi jariri

Image caption Za a dauki kwayoyin halittar uwa da na uba da kuma na wata mace daban

Burtaniya ta zamo kasa ta farko da za a dinga amfani da kwayoyin halittar mutane uku wajen kyankyasar jariri a kwalba.

'Yan majalisar dokokin kasar sun kada kuri'a da gagarumin rinjaye na amincewa da matakin wanda masana a fannin kimiyya suka ce zai kare yaduwar cututtukan da jariri zai iya gada daga mahaifiyarsa.

Firai ministan Burtaniya David Cameron ya ce zai goyi bayan sauyin don ya san yadda iyaye ke ji ganin shi ma kansa ya taba samun nakasashen da.

Sai dai kungiyoyin addinai da na masu fafutuka sun nuna adawa da matakin.