Sojojin Chadi da Kamaru sun kwato Gamboru

Sojojin Chadi Hakkin mallakar hoto
Image caption A baya sojojin Chadi sun kwato garin Malam Fatori

Rahotannin da BBC ta samu na cewa dakarun kasar Chadi da na Kamaru sun kwato garin Gamboru daga hannun Boko Haram.

Da safiyar ranar Talata ne dai sojojin Chadi da na Kamaru suka tsallaka zuwa cikin Nigeria ta kan gadar da ta raba Nigeria da Kamaru.

Wani dan gudun hijira da ke zaune a gain Fotokol na kasar Kamaru ya ce an kwashe sama da sa'a daya ana fafatawa tsakanin sojojin da kuma 'yan kungiyar Boko Haram.

Daga bisani dai fadan ya lafa, inda kuma wasu mazauna garin Fotokol, wanda bai wuce nisan kilomita 3 da garin Gamboru ba sun ce sun ga sojoji sun kama wasu da ake zargin yan kungiyar ta Boko Haram ne.

Kasar Chadi dai ta tura sojojinta zuwa Nigeria domin fatattakar yan kungiyar ta Boko Haram.

Dama a kwanakin baya an samu rahoton sojojinta sun kwato garin Malam Fatori daga hannun yan kungiyar Boko Haram.