2015: ICC ta yi gargadi a kan rikici a Nigeria

Image caption Fatou Bensouda ta ce Kotun za ta hukunta duk wanda ya tayar da rikici a Najeriya

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya-ICC ta ce wakilanta za su zo Najeriya domin ci gaba da tattauna wa da hukumomi a kasar domin ganin an kaucewa aikata manyan laifuka a lokacin babban zaben da kasar za ta gudanar, a watan Fabrairun da muke ciki.

Hakan kuwa yana kunshe ne a wata sanarwa da ofishin mai shigar da kara a kotun, Fatou Bensouda, ya fitar gabanin babban zaben kasar.

Sanarwar ta ce an gano cewa hamayya tsakanin 'yan siyasa ka iya haifar da manyan laifuka kamar kisan mutane da dama, kafin gudanar da zabe, da lokacin zaben, da ma bayan zaben.

Kotun ta ce tana da hurumin hukunta duk wani dan Najeriya da ya aikata manyan laifuka, a cikin kasar ko kuma a duk inda ya kasance a fadin duniya.

Ko a watan Janairun da ya gabata ma 'yan takarar shugabancin kasar sun rattaba hannu a kan wata yarjejniyar zaman lafiya, wadda tsohon magatakar Majalisar Dinkin duniya, Kofi Annan ya halarta.