Rufin mota ya yaye bayan ta doki bishiya

Hakkin mallakar hoto ETAHANAMEADE
Image caption Mutane biyu ne suka ji rauni sakamakon aukuwar lamarin.

Rufin wata mota ya yaye a London lokacin da ta yi karo da rassan wata bishiya a tsakiyar birnin.

Motar ta bus, mai lamba 91, ta doki rassan bishiyar ne a kan titin Kingsway, kusa da ginin makarantar London School of Economics (LSE) da ke yankin Holborn.

Jami'an da ke kula da zirga-zirga a birnin na London sun ce an kai mutane biyu asibiti sakamakon raunin da suka ji lokacin da motar ta yi hatsarin, koda yake sun ce raunin ba shi da girma.

An rufe titin na Kingsway lokacin da lamarin ya auku.