Ban Ki-moon ya zargi shugabannin Sudan ta Kudu

Ban Ki-moon Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ban Ki-moon yace matukar bangarorin biyu ba za su cire son zuciya ba, to zaman lafiya ba zai dore a Sudan ta Kudu ba.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya zargi shugabannin Sudan ta Kudu da son kan su fiye da bukatun jama'arsu.

Shugaba Salva Kiir da shugaban 'yan tawaye Riek Machar sun sake rattaba hannu akan wata yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar lahadi da ta wuce, amma sun gagara tattaunawa akan batutuwan da suka shafi kafa gwamnatiun hadin gwiwa.

Mr Ban ya yi kiran da su sake yarjejeniya mai dorewa , ya kuma ce babu zaman lafiyar da zai dore a Sudan ta Kudu matukar ba za su cire son zuciya ba.

Mr Machar ya shaidawa BBC cewa har yanzu bangarorin biyu na tattaunawa kan batun raba mulki a wani yunkuri na kafa gwamnatin hadaka.

Dubban mutane ne suka rasa rayukansu a yakin da ya barke tsakanin masu marawa Mr Kiir da Mr Machar baya a watan Disambar shekarar 2013.