Sojojin Chadi sun kashe 'yan Boko Haram 200

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dakarun Chadi na samun galaba a kan Boko Haram

Chadi ta ce ta kashe mayakan Boko Haram fiye da 200 a wata arangama da suka yi a garin Gamborou da ke kan iyakar Nigeria da Kamaru.

A nasu bangaren, hukumomin kasar Chadi sun ce an kashe musu sojoji tara, sannan aka raunata wasu 21 a tashin hankalin da ake ci gaba da fuskanta a wasu jihohin arewa maso gabashin Nigeria.

Sanarwar da sojin Chadin suka fitar ta ce har yanzu ana ci gaba da gumurzu domin murkushe ayyukan 'yan Boko Haram.

Dakarun Chadi kusan 2,000 ne suka shiga cikin Nigeria domin kawo karshen kashe-kashen da kungiyar Boko Haram ke yi.

Tun daga farkon wannan makon, dakarun Chadi suka soma kwato garuruwan da ke 'yan Boko Haram suka kwace a Nigeria.