Gawarwakin Sojojin Chadi sun isa Kamaru

Sojojin Chad Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Chad

Rahotanni daga Gamborou dake Jihar Bornon Najeriya na cewa gawarwakin sojojin Chadi 9 da aka kashe bayan wata arangama da suka yi da 'yan kungiyar Boko Haram a yankin Wungol da Ngala sun isa garin Fotokol dake Kamaru.

Artabun da dakarun hadin gwiwa ke yi da 'yan Boko Haram na ci gaba da tsananta tun bayan da kasar Chadi ta aika dakarunta zuwa kan iyakokinta da Nijar da kuma Najeriya.

Hakan ya baiwa dakarun Chadi damar karbo garin Gamborou da ya jima a hannun mayakan na Boko Haram inda bayanai ke cewa an kama da yawa daga cikin 'ya'yan kungiyar.

Karin bayani