'Yan Boko Haram sun kai hari a Fotokol

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mazauna Fotokol sun ce tun da asubahi 'yan Boko Haram ke bude musu wuta.

Wasu mutane da ake zargi 'yan Boko Haram sun kai hari a garin Fotokol na Jamhuriyyar Kamaru.

Garin dai yana kan iyaka ne da Najeriya.

Mazauna garin sun shaida wa BBC cewa 'yan Boko Haram din sun shiga garin ne da asubahin ranar Laraba, inda suka yi ta harbe-harbe.

Sun kara da cewa sojin Kamaru sun fafata da su, amma da alama har yanzu ba su kai ga murkushe su ba.

A cewarsu, yanzu haka an kona gidaje da dama, kuma mutane suna ta gudu domin tsira da rayukansu.