An kashe daruruwan 'yan Boko Haram a Fotokol

Hakkin mallakar hoto none
Image caption Sojojin Kamaru sun kashe 'yan Boko Haram a Fotokol

Rahotanni daga kasar Kamaru na cewa kimanin mutanen gari 80 ne suka mutu, sannan akalla wasu 120 suka samu raunuka a bata kashin da sojoji suka yi da 'yan kungiyar Boko Haram a ranar Laraba.

Bayanai sun nuna cewa kimanin mayakan kungiyar Boko Haram 1000 ne suka farwa garin, inda daga cikinsu aka kashe kimanin 600.

Wasu mazauna garin sun shaidawa BBC cewa sun banbance gawarwakin mutanen gari dana 'yan kungiyar ta Boko Haram ta hanyar kayayyinin dake jikkunan su, da kuma irin makaman da ke tare da su.

Mutanen suka ce sun bisne da yawa daga cikin gawarwakin mutanen gari, amma basu taba na mayakan kungiyar ba.

Rahotanni sun ce hukumomin Kamaru dana Chadi sun girke karin dakarun soji a Fotokol, domin dakile duk wani farmaki da mayakan kungiyar ta Boko Haram zasu nemi sake kai wa.