Jordan: Mun sa kafar wando daya da IS

Sarki Abdallah na Jordan Hakkin mallakar hoto
Image caption Sarki Abdallah na Jordan

Bayan ya gana da manyan jami'an soji da na tsaro, sarkin yace kasar za ta yaki kungiyar IS da kuma bin hakkin jinin Muath Kasasbeh.

Da yake magana a birnin Al-kahira, sakatare-janar na kungiyar hadin kan kasashen larabawa, Nabil al-Araby, ya yi Allah-wa dai da kisan, ya na mai cewa dole shugabannin duniya su dauki mataki don dakatar da munanan ayyukan IS.

A ranar Laraba kasar Jordan ta aiwatar da hukuncin kisa kan masu tada kayar baya guda biyu da ta ke tsare da su, don daukar fansa kan kisan Muath.